Hebrews 9

Sujada a cikin Wurin Kasancewa na Duniya

1Alkawari na farko fa ya kunshi ƙaʼidodi domin sujada da kuma domin wuri mai tsarki a nan duniya. 2An kafa Wurin kasancewa. A cikin ɗakinsa na farko akwai alkuki, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki. 3Saʼan nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki, 4wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma sandukin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin sandukin akwai tulun zinariya mai manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari. 5A bisa sandukin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu.
A alʼadance mazaunin jinƙai
Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.

6Saʼad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu. 7Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani. 8Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin Wurin kasancewa na fari yana nan tsaye. 9Wannan ma yana da maʼana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba. 10Waɗannan ƙaʼidodi sun shafi shaʼanin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙaʼidodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.

Jinin Kiristi

11Saʼad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin Wurin kasancewa mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba. 12Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. 13In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga alʼada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje, 14balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtace lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!

15Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari—yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yǎ ʼyantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.

16Saʼad da wani ya yi alkawari game da gādonsa,
Kalmar Girik guda da alkawari; haka ma a aya 17
dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta,
17domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai. 18Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini. 19Saʼad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hissof, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen. 20Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”
Fit 24.8
21Ta haka ya yayyafa jinin a kan Wurin kasancewa da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima. 22Hakika, doka ta bukaci a tsabtace kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.

23Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙaʼidodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau. 24Wannan ne ya sa Kiristi bai shiga wuri mai tsarkin da mutum ne ya yi wanda yake hoto ne kawai na ainihin ba. A maimakon haka, ya tafi cikin sama, yana kuma a can tare da Allah don yǎ taimake mu. 25Bai kuwa shiga sama domin yǎ yi ta miƙa kansa a kai-a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba. 26Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yǎ kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. 27Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yǎ mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shariʼa, 28haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yǎ ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yǎ ɗauki zunubi ba, sai dai don yǎ kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

Copyright information for HauSRK